TARIHIN SHEIK AMINU DAURAWA
Sunana Aminu Ibrahim bin Muhammad bin Bilal. Mahaifina shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai-Neman-Suna Fagge. Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa da tsohuwar tashar kuka. Tsawon shekaru arba’in, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa, bayan kasuwanci da sana’ar dinki, domin dogaro da kai. Sunan mahaifiyata Hajiya Sa’adatu Al-Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo. An haife ni a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32 unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala. Na fara karatun Alqur’ani mai girma tun ina dan karami, kuma na haddace shi a lokacin ina da shekara 14 zuwa 15. Bayan firamare da sakandare, da na yi, na kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyan mashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqur’ani da tafsir, wasu na Alqur’ani zalla, wasu na ilimi da fannoninsa daban-daban. Wadannan manyan malamai su ne: 1. Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa. 2. Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa. 3. Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa. 4. Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja. 5. Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda na yi gyaran tilawa a wajensa. 6. Sheikh Auwal Isa ‘Yan Tandu, wanda na yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa. 7. Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda na yi lugga da fiqihu da tafsir a wajensa. 8. Sheikh Idi Kajjin ‘Yan Awaki, wanda na yi hadith da lugga a wajensa. 9. Sheikh Zakari Mai littafi, wanda na yi lugga da fiqihu a wajensa. 10. Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda na yi nahawu da fiqihu a wajensa. 11. Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda na yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh a wajensa. Wannan malami, na yi tsawon shekara ashirin ina karatun ilimi a wajensa. Allah ya ji qansa da rahama! 12. Sheikh Abubakar Basakkwace Qoqi, wanda na yi fiqihu da lugga a wajensa. Wannan malami, a wajensa na sauke Alfiyya din Malik, da Muqamatul Hariri, da Shu’ara’ul Jahiliyya. Malami ne mai haquri da juriyar karantarwa. 13. Dr. Kabiru M. K. Yunus BUK, wanda na yi nahwu da lugga a wajensa. 14. Dr. Aminuddeen Abubakar, shugaban Da’awah, wanda na yi tauhidi da hadith a wajensa. 15. Dr. Ahmad Bamba BUK, wanda na yi hadith a wajensa. Wannan malami uba ne, kuma mai ba da shawara. 16. Dr. Abubakar Jibirin, wanda na yi Kitabut Tauhid a wajensa. 17. Sheikh Abdulwahab Abdallah, wanda na yi Musdalahul Hadith, da Qadarunnadah (nahawu), da Subulussalam (hadith) a wajensa. Wannan malami uba ne, kuma mai ba da shawara. Wadannan su ne malaman da na kwashe mafi yawan shekaruna ina zirga-zirga a tsakaninsu, wajen neman ilimi. Akwai wasu malaman da suka yi mini tasiri a rayuwa, amma ta hanyar karanta littattafansu da sauraren kaset-kaset dinsu: 1. Sheikh Muhammad bin Saleh Usaimin. Wannan malami ne, na kwashe tsawon shekara goma ina bin littattafansa da kaset-kaset dinsa na audio da bidiyo. Na tasirantu da shi kwarai da gaske. 2. Almuhaddith Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani. Wannan malami, duk littattafansa da suka fito kasuwa, da kaset-kaset, ina bibiyar su, saboda fa’idoji masu yawa. 3. Sheikh Bakar Abu Zaid. Saboda kwarewarsa a wajen sarrafa littattafai. Sauran su ne, Sheikhul Islam Ibni Taimiyya, da Sheikh Ibnul Qayyim, da Sheikhul Islam Azzahabiyy, da Sheikhul Islam Ibni Kathir, da Sheikhul Islam Ibni Hajar Al-Asqalani. Aqidata ita ce aqidar ahlussunnah wal jama’a. Ma’ana, imani da Alqur’ani da hadisan Manzon Allah (SAW) a kan fahimtar magabata na kwarai. Tsarin wa’azi: Tsakatsaki. Na ci gaba da karatu na zamani a Jami'ar Bayero, a bangaren jarida, Mass Comm. Wasu dalilai suka tsayar da ni. Na yi diploma a computer data processing. Iyali: A yanzu ina da mata biyu, da kuma ‘ya’ya tara. Daga cikin kasashen da na je domin wa’azantarwa, akwai Nijar, Togo, Ghana, Cote d’Voire. A jihohin Najeriya kuwa, babu jihar da ban je ba domin gabatar da wa’azi ko karantarwa.

Comments
Post a Comment
If this post is helpful. Drop us a message